<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><lyrics>[V1]
 1) Duk nufina da zuciyata, ya Allah, tone su.
 Asiran rai da tunani, ka auna su yanzu.

[V2]
 2) Mugun abu da tayarwa, ka taka, kashe su.
 Kada ka rage abu ɗaya mai musun ƙaunarka.

[V3]
 3) Inda na ƙi sarautarka a cikin raina dai,
 Amshi mabuɗi, shigo nan, ka share lolokai.

[V4]
 4) Kowane hali riƙaƙƙe da mugun tunani,
 Sarƙoƙin bautar Iblis ne, yau sai ka kwance su.

[V5]
 5) Maƃoya duk na tussan rai inda na ƙi ka da,
 Karƃi sarautarsu yanzu, Yesu Mai Mulkina.</lyrics>
<title>Duk Nufina da Zuciyata, Ya Allah, Tone Su LW39</title>
<hymn_number>39</hymn_number>
</song>